Kiwon Lafiya
Dillalan man fetur sun ce zai yi wuya su shigo da mai su sayar a farashin gwamnati
Dillalan man fetur da suke shigo da shi Najeriya sun ce ba mai yiwuwa bane su ci gaba da shigo da tataccen man fetur kuma su sayar da shi akan farashin naira dari da arba’in da biyar.
Shugaban kungiyar Dillalan man fetur na Najeriya Dapo Abiodun, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa ta Asorok jim kadan bayan kammala wani taro da suka yi da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari da kuma dukkan nin masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur.
A cewar sa indai har gwamnati na son farashin litar mai ya ci gaba da zama a naira dari da arba’in da biyar to kuwa ya zama wajibi ta nemo mafita.
Dapo Abiodun ya kuma ce a yanzu babu makawa ko dai gwamnati ta dawo da tallafin mai ko kuma ta samar da mafita wanda hakan ne kawai zai magance matsalar karancin man fetur.
Hakan na zuwa ne a daidai lokaci guda da gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti na musamman na masu ruwa da tsaki domin magance kalubale da ke addabar bangaren man fetur a kasar nan.
Akan hakan ne wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya jiyo mana ra’ayin mazauna birnin Kano.
Wasu mazauna birnin Kano kenan da ke bayyana ra’ayinsu kan kalaman da Dillalan man fetur su ka yi na cewa ba za su iya shigo da mai kuma su sayar da man akan lita dari da arba’in da biyar ba.