Labarai
Direbobin motocin dakon Fetur da Gas na shirin tsunduma yajin aiki

Ƙungiyar ma’aikatan dakon Man Fetur da Iskar Gas ta NUPENG, ta tabbatar da cewa za ta fara yajin aikin da ta sanar, daga yau Litinin, 8 ga Satumba.
Shugaban kungiyar ta NUPENG, Williams Akporeha, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ta cikin sanarwar, ƙungiyar ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta tuntubi NUPENG domin hana yajin aikin, amma hakan ba zai hana aiwatar da yajin ba, har sai bayan ganawar da za a yi da gwamnati a yau.
A cewarsa matakin ya samo asali ne daga shirin kamfanin Mai na Dangote na shigo da sabbin manyan motoci masu amfani da makamashin CNG guda 4,000 da za su rika kai mai kai tsaye zuwa gidajen Mai.
You must be logged in to post a comment Login