Labaran Kano
Dogaro da kai tsakanin matasa shi ne maganin rashin aikin yi
Kwamishinan matasa da raya al’adu na jihar Kano, Kabiru Ado Lakwaya ya ce kamata ya yi matasa su nemi na kansa tun da wuri, ba sai sun dogara da gwamnati ba.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne ta cikin shirin ’’Duniyanmu Ayau’’ na nan tashar Freedom radiyo, wanda ya maida hankali kan sana’oin hannu na matasan jihar nan.
Ya kara da cewa, tuni gwamnati ta himmatu don koyawa matasa sana’o’in hannu iri daban daban da nufin farfado da tattalin arzikin jihar nan, baya ga neman na kansu.
A na sa jawabin Kwamared Yahaya Sha’aibu Ungogo cewa ya yi, tuni gwamnati ta bai wa matasa sana’o’in da za su dogara da kansu, sannan ya yi kira da sarakunan gargajiya da su bullo da hanyoyin koyawa matasan sana’o’in hannu domin taimakawa kansu.
Shi ma wani wanda ya kasance cikin shirin Abdurazak Alkali cewa ya yi, matasanmu basa iya koyan sana’oin hannu da nufin taimakawa kansu, yana mai cewa, matasan kudu sun fi matasanmu na Arewacin kasar nan tashi tsaye wajen koyan sana’o’i.
Wakilinmu Shamsu Dau Abdullahi ya ce dukkanin bakin sun karkare da kira ga matasa da su maida hankali wajen koyan sana’o’in hannu don dogara da kansu.