Labaran Kano
Doka bata bawa jami’an tsaro damar haska fuskar wanda ake zargi da laifi ba- Masanin Doka
Wani masanin shari’a a Jami’ar Bayero dake nan Kano ya ce, kuskure ne babba yadda jami’an tsaro ke haska fuskokin mutanan da ake zargi da sunan sun aikata Laifi ba tare da an tabbatar da abin da ake zarginsu da shi ba.
Barriester Nuhu Isa Idris daga tsangayar koyar da shari’a na Jami’ar ta Bayero ne ya bayyana hakan.
Ya yi wannan batu ne yayin taron karawa juna Sani da cibiyar cigaban al’umma da wayar da Kai a nan Kano CDE ta shiryawa manema labarai a nan Kano.
Ya Kuma ce, idan har aka nuna fuskar Wanda ake zargi Kuma daga baya aka gano Bashi da Laifi an cutar da shi da Kuma iyalansa baki Daya.
You must be logged in to post a comment Login