Labarai
Dokar CBN bata shafi hada-hadar ko musayar kudi ta yanar gizo ba- Dr Abdussalam Kani
Wani Masanin tattalin arziki dake kwalejin Sa’adatu Rimi a nan Kano, Dr Abdussalam Muhammad Kani ya ce, dokar takaita cirar tsabar kudi a bankuna bashida alaka da ajiya ko musayar kudin a asusun banki ta yana gizo.
Dakta Abdussalam Muhammad Kani ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da Freedom Radio.
Wanda ya ce sabuwar dokar bankuna tsarine da zai taimaka ta hanyar kawarda barazanar rike manyan kudade a hannu mutane, ko ajiye su gidajen su.
Yana mai cewa dokar za kuma ta rage yawaitar kudaden jabu da suke yawo, dakuma koyardar halayyar ajiye kudi a bankuna tareda gudanar da hada-hadar kudaden cikin sauki ta hanyar aikewa dasu ta yana gizo.
Sai dai Dakta Kani yace, karancin bankuna a kasar nan zai iya haddasa hau-hawar farashi dama cinikin naira kamar cinikin dala sanadiyar wannan doka.
You must be logged in to post a comment Login