Connect with us

Labarai

 Dokar kare haƙƙin yara ta tsallake karatu na biyu

Published

on

Dokar kare haƙƙin yara, ta tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dokokin jihar Kano.

Dokar ta kai wannan mataki ne a zaman majalisar na Litinin din nan bayan da aka yi mata karatu na farko a ranar Talata.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne dai ya aike wa majalisar takardar neman yin nazari kan ƙudurin tare da sahalewa dokar.

Da yake karanto wasu daga cikin sassan da dokar ta ƙunsa, shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari, ya ce, dokar ta yi tanadin kare yara daga cin zarafi da wasu sauran batutuwa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!