Connect with us

Labarai

Gwamnati ta soke adaidaita ko a yi musu garambawul – Baffa Babba

Published

on

Hukumar Karota tace matukar gwamnati bata soke ci gaba da sana’ar tuka adaidaita sahu ba to kuwa ya Zama wajibi ta sauya tsarinsu.

Wanna dai ya biyo bayan matakin da suka dauka na tafiya yajin aiki.

Shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan a yau lokacin da gamayyar kungiyoyin baburan adaidaita sahu suka kai masu ziyara tare da nesanta kansu kan yajin aikin da ake tsaka da yi.

Ya ce kawo yanzu yana jiran hukuncin da gwamnatin Kano zata dauka akan abunda masu baburan adaidaita sahu suka yi.

A nasa bangaren shugaban gamayyar kungiyoyin matuka baburan Adaidaita Sahu na Kano Alhaji Mansur Tanimu kira yayi da gwamnatin da kada ta dauki mummunan mataki akan ‘yayan ta sakamakon rashin da’a da wasu daga ciki suka aikata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!