Labarai
Sabuwar dokar cirar kudi a Nijeriya zata taimaka wajen inganta tattalin arzikin ta-Dakta Kani
Wani masanin tattalin arziki da ke kwalejin Sa’adatu Rimi a nan Kano, Dakta Abdulsalam Muhammad Kani ya ce, dokar takaita cirar kudade a bankuna da babban bankin kasa CBN ya fito da ita, za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.
Dakta Abdussalam Kani ya bayyana haka ne a zantawarsa da Freedom Radio
Dakta Abdussalam Kani ya kara da cewa, sabuwar dokar bankunan zata kawar da barazanar rike manyan kudade a hannun al’umma ko ajiye su a gida, tare da gudanar da hada-hadar kudade cikin sauki.
Ya kuma ce dokar zata taimaka wajen hana satar kudaden gwamnati da kuma yaki da ayyukan ta’addaci a Najeriya.
Don haka yake shawartar al’umma dasu rungumi wannan tsarin na ajiyar kudi a bankuna, don gujewa matsalolin da aka iya zuwa, su dawo.
You must be logged in to post a comment Login