Labaran Kano
Dokar Zaɓe: Musa Iliyasu ya sauka daga Kwamishina
Kwamishinan raya karkara na Kano Musa Iliyasu Kwankwaso ya sauka daga muƙaminsa domin takarar ɗan majalisar tarayya.
A wata sanarwa da ya aike wa Freedom Radio, Musa Iliyasu ya ce, tsawon shekaru 24 ƙananan hukumomin Kura da Garin Malam ne ke wakiltarsu a tarayya, saboda haka yanzu lokaci ya yi da za a bai wa Madobi waje.
Musa Iliyasu ya ce, zai shiga a kara dashi a takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kura, Garin Malam da Madobi.
Kwankwaso ya ajiye muƙamin ne kwana guda bayan da Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya umarci masu riƙe da muƙaman siyasar da ke sha’awar takara su sauka, domin biyayya ga sabuwar dokar zaɓe.
Musa Iliyasu ya yabawa Gwamna Ganduje bisa bashi damar zama Kwamishina har tsawon shekara biyar.
Sannan yayi godiya ga mai ɗakin Gwamnan Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje, kan shawarwarin da yace tana bai wa Gwamna, da kuma gudummuwar da ta bashi.
Musa Iliyasu ya kuma bayyana cewa yana goyon Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a takarar Gwamna.
You must be logged in to post a comment Login