Connect with us

Coronavirus

Dr Ibrahim: Tsaftar muhalli ita ce mafita ga kamuwa daga Covid-19

Published

on

Shugaban Asibitin garin Danbatta Dakta Ibrahim ibn Muhammad ya bukaci al’umma dasu baiwa tsafta muhimmanci domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka masu yaduwa.

Dakta Ibrahim Ibn Muhammad ya bayyana haka ne a jiya a yayin taron fadakar da al’umma kan hanyoyin da ya kamata Su bi domin kare kansu daga annobar COVID-19 wanda kungiyar Indabawa Kurmawa Development Association ta shirya a yammacin jiya.

Likitan ya kuma ce tsaftar jiki da ta Muhalli har ma da ta abinci da kuma wanke hannu akai-akai ka iya taka rawa wajen kare kai daga kamuwa da cututtuka masu yaduwa, musamman amai da gudawa.

Da yake jawabi Shugaban kungiyar Indabawa Kurmawa Development Association Malam Aminu Shareef Dikko ya ce makasudun shirya taron, shi ne fadakar da al’umma musamman wadanda har yanzu basu amince da cutar Covid-19 ba.

Likitoci da dama sun gabatar da jawabai, inda suka bukaci al’umma dasu ringa bada ta zara a yayin mu’amalarsu da juna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!