Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

JAMB Ta saki sakamakon da ake dako

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta baiwa daliban da suka zauna jarrabawar shekarar 2020 damar fitar da sakamakon su na jarrabawa, Wanda aka dakatar sakamakon barkewar annobar Cobid-19.

Hakan na cikin mujallar da hukumar ke fitarwa a duk mako, mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar Dakta Fabian Benjamin.

JAMB ta saki sakamakon jarabawar UTME na bana

Har yanzu bamu tsayar da makin samun gurbin shiga jami’a ba -JAMB

Ta cikin sanarwar da hukumar ta fitar a jiya Lahadi ta kuma bayyana cewa, a yanzu haka kowanne dalibi zai iya fitar da sakamakon jarrabawar sa a shafin hukumar na website, bayan da hukumar ta aikewa da daliban sakamakon su ta wayar hannun tun da fari.

Sanarwar ta kuma ce, hukumar ta (JAMB) tayi wani zama na musamman ta internet da shugabannin jami’o’in kasar nan, don fitar da nagartaccen tsarin da za’a bi wajen baiwa dalibai gurabe, duk da yadda ake fama da annobar ta Covid-19.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!