Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

DSS ta kama gawurtattun yan fashi guda shida

Published

on

Hukumar tsaro ta DSS, ta ce, ta samu nasarar kama wasu gawurtattun ‘yan fashi da makami guda shida a garin Gegu Beki da ke kan hanyar Lokoja zuwa Abuja a jihar Kogi.

Wadanda DSS din ta kama bisa hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun hada da Kanal A.U. Sulaiman mai ritaya da Barista M.K. Aminu da Kabir Abdullahi, sai Isah Umar da Kadir Echi da kuma Adama Abdulkarim.

DSS din ta samu makamai da dama a hannunsu da kuma kudi.

Haka zalika DSS din ta samu nasarar cafke wani mai garkuwa da mutane mai suna Haruna Adamu a Jihar Adamawa, da wani mai sayawa ‘yan bindiga makamai mai suna Aminu Ibrahim, a kan hanyar Kubwa da ke birnin tarayya Abuja.

Sai wani mai suna Babangida Ibrahim da ke kai wa ‘yan bindiga a Jihar Zamfara makamai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!