Labarai
DSS ta saki Fulani 3 da ta kama bisa zarginsu da ta’addanci

Humumar tsaron farin kaya ta DSS ta saki wasu mutane uku Fulani da ta kama yayin da suke sauka daga jirgi bayan sun dawo daga aikin Hajji a watan yunin 2024
DSS ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a shalkwatar ta da ke Abuja inda ta ce, ta kama mutanen ne bisa zargin su da hannun a ayyyukan yin garkuwa da mutane a yankin arewacin Najriya.
Wadanda hukumar ta kama sun hadar da Rabi’u Alhaji Bello da Umar Ibrahim da Bammo Jajo Sarki, wadanda dukan su yan jihar Kwara ne.
Hukumar ta DSS ta ce, ta kammala bincike a kan su kuma ba ta same su da laifin komai ba, don haka ta bai wa kowannen su kyautar naira miliyan daya.
Kungiyoyin Fulani dai sun sha kokawa kan kama mutanensu game da zargin garkuwa da mutane da kuma ta’adanci ba tare da wata hujja ba inda suka ce hakan abin takaici ne.
You must be logged in to post a comment Login