Labarai
ECOWAS ta amince da John Mahama a matsayin ɗan takarar Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika (AU)

Majalisar Ministocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta amince da Shugaban Ghana, John Mahama, a matsayin ɗan takarar kungiyar da zai nemi kujerar Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) a shekarar 2027, lokacin da jagorancin zai koma yankin Yammacin Afrika.
An cimma wannan matsaya ne a taron ministocin karo na 95 da aka gudanar a babban birnin tarayyar Najeria Abuja, inda aka bayyana Ghana a matsayin muhimmiyar ƙasa a ECOWAS wadda ke ba da gudunmuwa ga martabar ƙungiyar a matakin duniya.
Jaridar Premium Times ta ambato Ministan Harkokin Wajen Ghana, Sam Ablakwa, ya bayyana cewa shugabannin kasashen ECOWAS za su tabbatar da wannan matsaya a gobe Lahadi.
You must be logged in to post a comment Login