Labarai
ECOWAS ta bayyana damuwa kan harin soji da gwamnatin shugaba Trump ta kai Venezuela

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta bayyana damuwa kan harin sojin Amurka da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta kai a Venezuela.
A wata sanarwa da ta fitar a Abuja, ECOWAS ta amince da haƙƙin kowace ƙasa na yaƙi da manyan laifukan ƙasa da ƙasa kamar ta’addanci da safarar miyagun ƙwayoyi, amma ta jaddada cewa dole ne a aiwatar da hakan bisa ƙa’idojin dokar ƙasashen duniya da kuma mutunta ikon ƙasashe masu cin gashin kansu.
Kungiyar ta tunatar da al’ummar duniya wajibcin mutunta cikakken ikon ƙasa da yancinta, kamar yadda Sashe na 2(4) na Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya ya tanada, wanda ke hana amfani da ƙarfi ko barazanar amfani da ƙarfi kan wata ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login