Connect with us

Labarai

ECOWAS ta koka kan yadda kasashen kungiyar basa aiwatar da hukuncin da kotu ta yanke

Published

on

Shugaban kotun kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, mai sharia Edward Amoako Asante ya nuna takaicin sa kan yadda kasasshen dake cikin kungiyar ba sa aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke.

Amoako ya bayyana haka ne lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wajen bude sabon ofishi a birnin tarayya Abuja, in da ya ce kaso 30 ne kadai na hukuncin da suka yanke ake aiwatar wa.

A cewar sa kotun na taka muhimmiyar rawa wajen abinda ya shafi samar da zaman lafiya da gwamnati ta gari da kuma gudanar da komai yadda yakamata a yankin.

Asante ya kuma tabbatar da cewar za su ci gaba da bada tasu gudunmuwar da ta kamata ganin yadda kotun ke zama babban tubali a kungiyar ta ECOWAS.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!