Connect with us

Labarai

EFCC ta kafa sashen sa ido kan kuɗaɗen jihohi don daƙile cin hanci

Published

on

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa a Najeriya (EFCC) ta ce ta kafa wani sashe na musamman da zai riƙa sa ido kan shigar da fitar kuɗaɗen gwamnatocin jihohi a wani ɓangare na ƙoƙarinta na hana cin hanci da sauran laifukan kuɗi.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyode, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wata maƙala ta musamman domin murnar cika shekaru 30 da kafuwar jihar Zamfara a birnin Gusau.

Ya ce a yanzu EFCC tana mayar da hankali wajen hana afkuwar laifukan kuɗi tun kafin su faru, maimakon taƙaita aikinta ga gurfanar da masu aikata laifuka bayan an wawure kuɗaɗen gwamnati.

A cewarsa, sabon sashen da aka kafa zai riƙa bibiyar harkokin kuɗaɗen gwamnatocin jihohi domin hana karkatar da dukiyar alʼumma da kuma almundahanar kuɗaɗen gwamnati.

Olukoyode ya ce matakin na da nufin inganta gaskiya, riƙon amana da kuma tabbatar da ana tafiyar da kuɗaɗen alʼumma yadda ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!