Labarai
EFCC za ta kama masu yi mata sojan gona a social media

Hukumar da ke hana cin hanci da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC ta ce za ta fara kama mutanen da ke amfani da sunanta ko tambarinta a wasannin kwaikwayo ba tare da izini ba.
Hakan na kunshe cikin wani sakon bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook da safiyar Asabar, dauke da alamar gargadi ga jama’a a rubuce.
A cikin sanarwar, hukumar ta nuna takaici kan yadda ake amfani da sunanta, tambarinta ko kakin jami’anta a wasannin barkwanci da bidiyoyin sada zumunta domin neman suna ko mabiya, inda ta ce hakan laifi ne kuma bata suna ne.
EFCC ta kara da cewa ta lura da yadda ake amfani da sunanta ko tambarinta a irin wadannan shirye-shirye ba tare da izini ba, lamarin da ya sabawa doka.
A karshe, hukumar ta gargadi jama’a da su guji hakan, tana mai cewa za ta fara kama duk wanda aka samu da aikata irin wadannan laifuka tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login