Labarai
Kotu ta yi watsi da kofarin Lauyan tsohon gwamnan Kogi Yahya Bello

Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙorafin lauyan kariya a shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Adoza Bello, kan zargin badakalar kuɗi ta naira biliyan 80.2.
Alƙalin kotun, Emeka Nwite, ya ce ƙorafin da lauyan kariya J.B. Daudu (SAN) ya gabatar ba shi da tushe, inda ya amince a ci gaba da shari’ar.
Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) na tuhumar Bello da laifuffuka guda 19 da suka shafi zargin wankin kuɗi.
A zaman kotun na ranar Juma’a, masu gabatar da ƙara sun ci gaba da gabatar da shaidarsu ta 12, Jamilu Abdullahi, ɗan kasuwar canjin kuɗi (BDC).
Shaidar ya bayyana cewa ya gudanar da mu’amaloli na canjin kuɗaɗe da wani Abba Adaudu, inda ya ce a wasu lokuta ana ba shi kuɗin dala a hannu domin aiwatar da canje-canje ko biyan wasu kuɗaɗe.
Ya kuma ce an ba shi dala dubu 300 a hannu domin biyan kuɗin makarantar Zahra da Fatima Bello, kuma ya taimaka wajen aiwatar da canja wurin kuɗin.
A yayin tambayoyi daga ɓangaren kariya, shaidar ya tabbatar da cewa ya bayar da bayani ga EFCC a ranar 10 ga Mayu, 2022.
Alƙali Nwite ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranakun 6 da 7 ga Mayu, 2026, domin ci gaba da shari’ar
You must be logged in to post a comment Login