Connect with us

Labarai

Sojoji sun kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Filato

Published

on

Sojojin Najeriya sun ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su tare da lalata wasu sansanonin ’yan bindiga yayin wani samame da suka kai dajin Daji Madam da ke tsakanin Ƙananan Hukumomin Wase da Kanam a Jihar Filato.

Majiyoyin soji sun ce farmakin ya mayar da hankali ne kan sanannun maɓoyar ’yan bindiga da suka haɗa da Dogo Ruwa da Bogwas.

An ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan yawaitar hare-hare, sace-sacen da kashe-kashe ga mutane a Wase da Kanam, inda mazauna yankin da jami’an tsaro da ’yan banga da dama suka rasa rayukansu.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Waziri Usman, ya ce ya shafe kwanaki 13 a hannun masu garkuwa da mutane bayan an sace shi tare da wasu yayin da suke dawowa daga aikin gawayi.

A cewar sa sun kai su cikin daji a kan babura, inda suka yimusu duka sannan suka hana su abinci, kuma suka basu gurbataccen ruwa.sai kuma suka nemi kuɗin fansa har Naira miliyan 30, in ji shi.

Ya ce sun samu damar tserewa ne lokacin da sojoji suka tsananta kai farmaki tare da jiragen yaƙi suna shawagi a sama, lamarin da ya tilasta wa ’yan bindigar tserewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!