Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mai yuwa a sake samun barkewar cutar Corona – Boss Mustapha

Published

on

Gwamnatin tarrayya ta yi gargadin ce mai yuwa ne za’a sake samun barkewar cutar Corona a kasar nan muddin aka dakile cigaban da aka samu.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya sanar da hakan ya yin da yake kaddamar da kwamitin kwararru karkashin shirin bincike a bangaren lafiya da bunkasa ayyuka ta kasa a yau Abuja.

Boss Mustapha ya ce muddin muka yi wasarirai da damar da muka samu, ba abu ne mai wuya ba mu sake koma baya wajen samun karuwar masu dauke da cutar COVID-19.

Labarai masu alaka : 

Corona ta sake bulla a jihar Zamfara

Har yanzu bamu farfado daga mashash-sharar Corona ba – Masu kananan sana’o’i

An samu karin masu Corona 643 a Najeriya

Sakataren gwamnatin tarraya ya kara da cewar,cutar Corona ta fallasa matsalolin da muke samu a bangaren kiwon lafiya, a don haka akwai bukatar mu sake zage damtse wajen daukar matakan kariya kan cutar ta Korona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!