Connect with us

Labarai

El-Rufai ya gurfana a gaban kotuna biyu kan zargin almundahana

Published

on

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gurfana a gaban kotuna biyu a jihar ranar Laraba kan tuhume-tuhumen da suka shafi zargin almundahanar kuɗi, amfani da mukami ba daidai ba da kuma wanke kuɗaɗe.

A Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, El-Rufai ya gurfana tare da tsohon mai ba shi shawara na musamman, Jimi Lawal, da wasu kamfanoni biyar kan sabbin tuhume-tuhume guda 11 da Hukumar ICPC ta shigar.

Yayin zaman kotun, El-Rufai da Lawal sun musanta zarge-zargen da ake yi musu.

Lauyoyinsu sun nemi a ba su beli, yayin da mai shari’a Hauwa’u Buhari ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar belin zuwa ranar 1 ga Yulin 2026.

Bayan kammala zaman a kotun tarayya, El-Rufai ya sake bayyana a Babbar Kotun Jihar Kaduna domin ci gaba da sauraron wata shari’a ta daban da ICPC ta shigar a kansa.

Wannan shari’ar na da alaƙa da zargin amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba da kuma wanke kuɗaɗe.

Bayan taƙaitaccen zama, kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga Yunin 2026.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!