Connect with us

Labarai

Gwamna Abba ya kafa kwamitin bincike kan rasuwar ɗalibar St. Louis

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin mutuwar ɗalibar makarantar sakandare ta St. Louis da ke  jihar.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na jihar kano ,Dakta Gwani Ali Haruna Makoda, zai gudanar da cikakken bincike kan yadda lamarin ya faru.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta ce kwamitin zai kuma binciki zarge-zargen cin zarafi, gallazawa ko hukunci ba bisa ƙa’ida ba da ake zargin wasu ɗalibai sun yi, tare da daukar matakan hukunta duk wanda aka samu da hannu.

Ana sa ran kwamitin zai miƙa rahotonsa ga gwamnati cikin wa’adin da aka tsara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!