Labarai
Gwamna Abba Kabir zai gana da dukkan jami’an gwamnatinsa

Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya gayyaci dukkan zababbun da nadaddun jami’an gwamnatin jihar zuwa wata muhimmiyar ganawa a Yau Alhamis.
Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Sanarwar ta ce za a gudanar da ganawar da karfe 1 na rana a ɗakin taro na Coronation da ke Gidan Gwamnatin Kano.
Wadanda aka gayyata sun hada da ƴan Majalisar Dokokin Jihar Kano na APC, shugabannin kananan hukumomi, kwamishinoni, masu ba da shawara, da mataimaka, shugabannin hukumomi da masu ɗaukowa gwamnan rahoto da sauran jami’an gwamnati.
Sanarwar ta ce tilas sai wadanda aka gayyata sun zo da katin shaidar aiki domin samun damar shiga wurin ganawar.
You must be logged in to post a comment Login