Connect with us

Labarai

Kwanci-tashi: Masu Corona 26 suka rage a Kano

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ce a yanzu haka mutane 26 ne suka rage masu fama da cutar Corona a Jihar, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Jihar ta wallafa a shafinta na tiwita a daren jiya.
A jiyan dai mutum guda ne ya kamu da cutar bayan gwajin da aka yi wa mutane 130, inda kuma aka sallami mutane 27 daga cibiyar killace masu fama da cutar bayan sun warke.
Mutane 126 ne dai suka kamu da kwayar cutar jiya a fadin kasar nan kamar yadda cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta wallafa a shafinta na tiwita.
Cibiyar ta ce mutane 56,604 suka kamu da cutar inda aka sallami 47,872 bayan sun warke, to amma 1,091 sun rasu a anadiyyar cutar a kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,636 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!