Connect with us

Labarai

Ganduje ya jajanta wa wadanda iftila’in rusau ya shafa a Kano

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci Unguwar kofar Mazugal, Lungun mai lalle, don jajantawa wadanda iftila’in rusau ya afkawa a cikin makon nan.
Gwamnan na Kano wanda mataimakinsa Alhaji Nasir Yusuf Gawuna ya wakilta ya ce hakika wannan al’amari abin jajantawa ne.
Mutane goma sha takwas ne dai iftilai’n na rusau ya afkawa inda kuma yara biyu suka rasa rayukansu a Unguwar ta Kofar Mazugal, Lungun mai lalle.
Da yake jawabi yayin ziyarar kwamandan hukumar Hizba ta Jihar Kano Sheikh Harun Ibn Sina, ya buka ci mutanen su dauki wannan lamari tamkar jarrabawa daga ubangiji, tare da addu’a ga mamatan da suka rasu.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa mataimakin gwamnan ya samu rakiyar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kano, inda kuma aka kai kayan abinci da kudi da kuma kayan gini.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 331,696 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!