Labarai
El’rufa’i ya sake gurfana a kotu da safiyar yau Talata

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El’rufa’i ya gurfana a gaban babbatar kotun tarayya dake Kaduna da safiyar yau Talata.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC dai ce ta shigar da tsohon gwamnan kara bisa zarge zarge 10 da take tuhumar sa.
An gabatar da tsohon gwamnan a kotu bayan ya shafe sama da wata guda a tsare, a hannun hukumar, da a baya baya nan ya yi kwanaki Hudu a Abuja, karbar Ta’aziyyar mahaifiyar sa da ta rasu kafin sake gufaranar da shi a kotun da safiyar yau karkashin mai shari’a Rilwan M. Aikawa.
You must be logged in to post a comment Login