Labarai
EndSARS : Ya yi hanzari kirkiro SWAT – Kungiyar Gwamnoni
Gwamnonin kasar sun ce kirkiro rundunar SWAT bayan rushe runduar yaki da ‘yan fashi da makami ta SARS ya yi hanzari.
Gwamnonin sun kuma bukaci babban sefeton ‘yan sanda ta kasa Muhammad Adamu ya gaggauta gudanar da taro da masu ruwa da tsaki don samar da mafuta.
Jaridar THE NATION ta rawaito cewa gwamnonin sun bayyana matsayin su ne cikin takardar bayan taro da suka fitar da suka kammala a babban birnin tarayya Abuja.
Takardar bayan taron wanda shugaban kungiyar gwamnoni Dr, Kayode Fayemi ya sanya wa hannu cewa, babban Sepeton ‘yan sanda ya shedawa kungiyar gwamnonin matakan da rundunar ‘yan sandan zata dauka.
Akasarin masu zanga-zanga da suka gudanar a sassan kasar nan sun ki amincewa da rundunar SWAT suna mai cewa a fakaice SARS ce zata dawo.
Sai dai babban sefeton ‘yan sanda na kasa Muhammda Adamu ya bada tabbacin cewa babu wani jami’in dan sanda da ya yi aiki a rundunar SARS da kuma zai cigaba da aiki a SWAT.
You must be logged in to post a comment Login