Connect with us

Kimiyya

Erdogan’s Revenge

Published

on

President Recep Tayyip Erdogan has responded to the failed coup in Turkey with indiscriminate retribution. At last count, nearly 35,000 members of the military, security forces and judiciary — including 103 generals and admirals — have been detained or dismissed; 15,000 education ministry employees have been suspended; the licenses of 21,000 teachers have been revoked; and more than 1,500 university deans have been forced to resign.

The purge is stunning in its breadth and depth, extending into the political and business classes as well as the government. How many of these people were actually involved in the weekend mutiny against Mr. Erdogan is unclear. Also unclear is whether Turkey’s fragile democracy can survive this challenge, whether it will become a kind of de facto authoritarian state and — of deep interest to Washington — whether it can recover sufficiently to continue on as a credible member of NATO, the alliance’s eastern anchor.

At such a time, one would hope for a leader willing and eager to unify his people under the rule of law, to reaffirm democratic values and to address the grievances that motivated the plotters in the first place. So far, Mr. Erdogan seems determined to fail this test of leadership.

Since the coup attempt, he has raised the prospect of reinstating the death penalty. After many terrorist incidents, he told CNN, the Turkish people seem amenable to the idea that “terrorists should be killed.” But of course any blood bath sanctioned by the government would destabilize Turkey further and seal Mr. Erdogan’s legacy as the man who destroyed modern Turkey’s promise as a model Muslim democracy.

The coup attempt seems to have magnified the authoritarian behavior bordering on paranoia that has increasingly come to define Mr. Erdogan’s leadership. In recent years, he has seized control of media outlets and lashed out at enemies real and imagined. He said the coup was the responsibility of Fethullah Gulen, a Muslim cleric living in Pennsylvania who used to be an ally until a falling out three years ago, and the government has demanded his extradition.

The Obama administration says it will consider this request if corroborating evidence is provided. Behind the scenes as well as publicly, the administration has made clear that it condemns the coup and that the two allies, often at odds, must remain committed to the fight against the Islamic State.

One unanswered question is what to do with NATO tactical nuclear weapons at Incirlik air base in southeast Turkey. The base commander and several other Turkish officers there have been detained for reportedly supporting the insurrection. American officials say the weapons are secure and they are not planning to relocate them.

The administration and the European Union have been walking a careful line, emphasizing support for Turkey while also encouraging Mr. Erdogan to follow the rule of law and other principles that unite Turkey and Europe. The people who filled the streets on Saturday to condemn the coup did so to protect constitutional democracy as much as to defend Mr. Erdogan. He would be wise to heed that message.

Culled from The New York Times

Kimiyya

Za’a fara amfani da fasahar zamani don inganta noma- AATF

Published

on

Shugaban kungiyar harkokin noma ta Afirka AAFT Dr Issuofou Kollo Abdourhamane ya ja hankalin kasashen Afirka wajen yin maraba da sabbin hanyoyin fasaha a matsayin wata hanya da za’a magance matsalolin karancin abinci da ke tunkarar nahiyar Afirka.

 

Dr Abdourhamane ya bayyana haka ne a yayin taron karawa juna sani na yan jaridu mai taken South west Agroecological ‘ da aka gudanar a jamiyar Obafemi Awolowo.

 

Ya ce  wannan wani cigaba ne da ake samu ta hanyar fasaha, na samar da muhalli mai ingance ba tare da an gurbata shi ba.

 

Afirka zata iya samar da tsaftaccen abinci tare da magance matsala ta fari da yunwa da ka iya faruwa muddin ba’a samar da hanyar inganta samar da abinci ba.

 

Yana mai bayyana nau’ikan abincin da ka iya karanci a nahiyar Afirka sakamakon gurbatar yanayi ta hanyar wasu sinadaran da ke kashe albarkar kasa , ko magungunan kwari da wasu kamfanoni ke fitarwa ga muhalli.

 

A yanzu haka dai nahiyar Afirka musammam kasashen  ke da sahara na gab da fuskantar rashin isasshen abinci.

 

Ya ce rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO  ta ce akalla kimanin fiye da yara miliyan 8 ne ke fama da yunwa , wanda adadinsu ya kai kimanin kaso 48 cikin dari dari na adadin lafiyayyun yara da ake da su a nahiyar Afirka a wannan karni.

 

Dr Issouffou ya ce amfani da fasaha ne kadai zai magance matsalolin da zasu magance fari da yunwa wanda kungiyar AATF ke aiki tukuru akan ta.

 

Ya kara da cewa tun da suka fara ayyuka a fannin cigaba na samar da abinci a Najeriya sun samar da ingantaccen irin rogo wanda ya taimakawa manoma samar da rogo na kimanin fiye da tan 32 a shekarun da suka gabata.

 

A yanzu haka suna kan aiki akan sarrafa noman shinkafa da inganta irin waken da kwari basa ci.

 

 

Da yake jawabi shugaban jami’ar ta Obafemi Owolowo farfesa Eyitope Ogungbenro Ogunbodede ya ce taron ya zo a lokacin da ake bukata, domin gwamnati na yunkurin tabbatar da abinci ya wadata a kasa baki daya

 

A hannu guda kuma gwamnati na kokarin samar da  hanyar kudaden shiga.

 

Ya ce Najeriya na da adadin alumma da suka kai fiye da miliyan 170 , hakan ce ta sa samar da abinci ke da muhimmanci .

 

Ko a maganar da ake yi nan ba da jimawa ba gwmanatin tarayya tana dab da sayar da irin waken da kwari basa ci.

Continue Reading

Kasuwanci

An fara kera Fensir a Najeriya

Published

on

Wani kamfani a nan  gida Najeriya ya fara kera fensira ta hanyar amfani da tsaffin jaridu .

 

Ministan kimiyya da fasaha Dr. Ogbonnaya Onu ne ya bayyawa cewar kamfanin zai fara samar da akalla pensira fiye da miliyan biyu a duk shekara wanda ya fi karfin amfani birane da yankuna kadai.

 

Da yake Magana jiya a Abuja yayin da ya karbi bakuncin gangun wani kamfanin da ke samar da pensira na Bamib ya ce’ mun yaba da yadda kake gudanar da ayyukanka na cigaban kasa.

 

Ya ce a wata ziyara da suka kai wani kamfanin samar da fensira a jiha Enugu , ‘mun tarar da su suna gudanar da bincike akan fensira, abin takaici ne sakamakon kasar nan bata da wani kamfani da ke samar da fensira a Najeriya .

 

A da akwai wasu kamfanunuwa da suke sarrafa fensira amma dukkaninsu sun dakushe a yanzu, hakan ce ta sa a matsayina na ministan kimiyya da fasaha na ga dacewar sarrafa shi a Najeriya duba da yadda daliban mu na firamare da ma wasu yan sakandare da ke amfani da fensir.

 

Minister Onu ya ce a ganinsa fensir ba wani a zo a gani ba, ya kuma zama wajibi a ce Najeriya tana samar da fensiran da take amfani da su.

 

Ya ce mun basu shekara biyu domin samar da adadin fensiran da ake bukata, yana mai cewa samar da fensiran ya dauki hankali na, domin kuwa duk kayayyakin da ake kera fensiran muna da shi a Najeriya, hakan dai zai samar da ayyukan yi ga matasa

 

Ministan ya ce kawo yanzu an samu cigaba domin zasu tabbatar da cewar an samar da dukkanin kayayyakin a nan gida Najeriya, tare da cewar tuni gwamnatin Akwa Ibom suka fara kira fensira wanda wannan wani cigaba ne.

Continue Reading

Kimiyya

Yadda iPhone 11 ta yamutsa hazo a soshiyal midiya

Published

on

Yadda iPhone 11 ta yamutsa hazo a soshiyal midiya

A ranar 10 ga watan Satumban da muke ciki ne kamfanin sarrafa na’urorin sadarwa na zamani wato Apple ya kaddamar da sabbin kayayyaki, ciki harda wayoyin iPhone 11, iPhone II Pro da kuma Pro Max, wato dai zafafan wayoyi guda uku daga kamfanin.

Wadannan wayoyi dai sun kunshi wasu abubuwa na musamman wadanda suka yiwa sauran wayoyi zarra, an gina kwakwalwar iPhone 11 akan A13 Bionic, a bangaren karfin ma’ajiyar bayanai kuwa wato Memory ta fara daga 64GB, 256GB, da kuma 512GB.

A bangaren kyamara (camera) kuwa iPhone 11 tana da girman 12PM + 12PM, baki dayan kyamarar wayar kuwa iPhone 11 tazo da kyamara guda biyu (2) yayin da iPhone 11 Pro da Pro Max suka zo da kyamara guda uku, wadannan wayoyi dai sune kan gaba wajen karfin kyamara a halin yanzu a duniya.

Game da girman jikin kuwa wayoyin sun kai inci 5.94 x 2.98 x 0.33, babu maganar rashin rike caji domin kuwa an yiwa wadannan wayoyi kyaky-kyawan shiri wajen rike caji na tsawon lokaci.

Akwai wayoyin iPhone 11 kaloli da dama wadanda suka hadar da Fara, Baka, Ruwan Dorawa, Koriya, Ja da kuma Ruwan Hoda.

A ranar 20 ga watan Satumban da muke ciki ne dai aka fara sayar da iPhone 11 akan kudi dalar Amurka $3600 wanda ya kama N252, 000 a kudin mu na nan gida Najeriya.

An kafa kamfanin Apple ne a watan Afrilu na shekarar 1987, a birnin California na kasar Amurka, a yanzu dai yana daya daga cikin manyan kamfanonin kere-keren fasahar zamani dake jan zare a duniya.

 

A nan gida Najeriya wayar iPhone ta zamo wata abar alfahari ga al’umma, musamman matasa wanda kowa ke ribibi wajen ganin ya mallaki waya kirar kamfanin, hakan ne ya sanya labarin kaddamar da iPhone 11 ya zamo jigon tattaunawa a shafukan sada zumunta, inda matasa suka dinga wallafa bayanai kala-kala akan wannan wayar, hakan yasa muka leka dandalin sada zumunta na Twitter da kuma Facebook inda muka dauko muku wasa daga tattaunawar da matasan keyi.Ku bayyana mana ra’ayoyin ku dangane da iPhone 11.

 

Basheer Sharfadi

23rd, September, 2019.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 324,535 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!