Ƙetare
Eritrea ta fice daga kungiyar kasashen Gabashin Afirka IGAD

Kasar Eritrea ta sanar da ficewarta daga kungiyar kasashen Gabashin Afirka ta IGAD, tana mai zargin kungiyar da fatali da ka’idojin da aka kafa ta a kai da kuma gaza taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
A cewar ma’aikatar harkokin wajen Eritrea, wadda ta fitar da bayanin ta cikin wata sanarwa ta ce kasar bata karuwa da kasancewarta karkashin kungiyar, musamman a bangaren samun aminci da zaman lafiya.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da musayar kalamai masu zafi tsakanin Eritrea da makwabciyarta Habasha, lamarin da ke kara tayar da hankula a yankin.
You must be logged in to post a comment Login