Labaran Wasanni
Erling Haaland zai Kwashe makonni yana jinyar rauni

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund Erling Haaland zaiyi jinyar raunin da ya samu.
Mai horara da kungiyar, Marco Rose ne ya sanar da hakan a ranar Juma”a 22 ga Oktoban da muke ciki.
Mai shekaru 21 dan kasar Norway ya buga wasan da Dortmund ta yi rashin nasara da ci 4-0 a hannun Ajax a gasar cin kofin zakarun turai ta Champions league da ta gudana a ranar Laraba 20 ga watan na Oktoba.
“Lokaci ya yi da zan fuskanci raunin da naji, sakamakon rashin jin dadi da banayi, a cewar Haaland ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Haaland, dai kawo yanzu ya zura kwallaye tara a gasar Bundesliga da kawo yanzu ya ke gaban dan wasan Bayer Munich Robert Lewandowski a yawan zura kwallaye.
Ana saran dan wasa Haaland bazai buga wasanni 3 ba daga cikin wasanni da kungiyar sa za ta buga.Hakan kuma zai hana dan wasa Haaland wakiltar kasarsa a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya da kasashen Latvia da Holland a ranakun 13 da 16 ga watan Nuwamba mai kamawa.
Kasar Norway dai rabon ta da buga wata gasa a duniya tin gasar Euro ta shekarar 2000 da ta kammala a mataki na biyu a rukunin G da maki biyu kacal.
You must be logged in to post a comment Login