Labarai
EU ta baiwa Nijeriya tallafin Naira miliyan 75 don yaki da cutar Diphtheria
Kungiyar tarayyar turai EU ta baiwa Nigeriya tallafin Naira Miliyan 75 don yaki da cutar sarkewar numfashi wato Diphtheria a turance.
Asusun bayar da agajin zai taimakawa al’umma da abin ya shafa a jihohin Kano, Katsina, Legas, da kuma Osun.
A cikin wata sanarwa da kungiyar tarayyar turai da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka suka fitar, sun ce rabon tallafin ya biyo bayan yadda ake samun rahoton karuwar masu kamuwa da cutar diphtheria tun daga farkon shekarar 2023 da muke ciki.
Idan za a iya tunawa tun a ranar 20 ga watan Janairu 2023 ne, Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta tabbatar da bullar cutar diphtheria a hukumance a jihohin Kano da Legas bayan da wasu da ake zargin sun kamu da cutar sun shiga jihohin.
Rahoton:Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login