Labaran Wasanni
European Super League: FIFA bata san da yarjejeniyar Barcelona ba
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce bata san da akwai wata yarjejeniya tsakaninta da kungiyar Barcelona ba ta shiga sabuwar gasar kasashen nahiyar turai Super League.
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Josep Maria Bartomeu ya bayyana cewa Barcelona ta fara shirye-shiryen ta na Super League, yayin da yake jawabin ajiye aikinsa da kungiyar.
Bartomeu dai sauka daga shugabancin kungiyar tare da sauran hukumomin gudanarwa sakamakon cigaba da fuskantar barazanar tsigewa daga magoya bayan kungiyar.
A makon da ya gabata ne shafin wallafa labaran wasanni na BBC ya bayyana cewa ana cigaba da tattaunawa kan kirkirar sabuwar gasar firimiya da tsabar kudi Yuro biliyan 4.6 a nahiyar turai.
Manyan kungiyoyin kwallon kafa dake nahiyar ta turai zasu shiga gasar da aka fara tattaunawa ba da dadewa ba.
You must be logged in to post a comment Login