Kiwon Lafiya
Fadar shugaban kasa ta bukaci majalisar dattawa da ta janye haramci da ta yi
Fadar shugaban kasa ta bukaci majalisar Dattawa da ta janye haramcin da ta yi nakin tantancewa da kuma tabbatar da sunayen mutanen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya turo mata da su domin nadasu a matsayin mukamai daban-daban.
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin majalisar Dattawa Sanata Ita Enang ne ya bayyana hakan, lokacin da majalisar ke tantance wasu mutane da shugaban kasa ya turo da sunayen su domin nadasu a matsayin mukamai a babban bankin kasa CBN.
Ya ce, majalisar ta kyauta da ta gaggauta tantance mutanen shida, sai dai zai fi kyautatuwa idan ta gayyaci sauran mutanen da shugaban kasa ya turo gabanta domin suma a tantance su.
Wadanda majalisar Dattawan ta tantance a jiyan sun hada da: Aisha Ahmad da Edward Adamu wadanda aka tantance su don nadasu a matsayin mataimakan gwamnan babban bankin kasa CBN, yayin da kuma aka tantance farfesa Adeola Festus Adenikinju da Dr Aliyu Rafindadi Sanusi da Dr. Robert Chikwendu Asogwa da kuma Dr Asheikh Maidugu a matsayin mambobin kwamitin kudi na babban bankin kasa CBN.
A shekarar da ta wuce ne dai majalisar Dattawa ta ki tantance wasu mutane da shugaban kasa ya turo da sunayen su domin nadasu a mukamai daban-daban.
Rahotanni sun ce majalisar Dattawan ta dau wannan mataki ne jim kadan bayan kalaman da mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya yi game da kin tantance shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.