Labarai
Fadar shugaban kasa:ba’a yi wa Buhari adalci ba kan shuka mara ma’ana kan sake zabe a wasu jihohi
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewar, ba’a yi wa shugaban kasa Muhamamdu Buhari adalci ba, kan shuka mara ma’ana da ake wa shugaban kasa Muhamamdu daban-daban kan zaben da za’a sake yi a jihohin da ba’a kammala zabe ba.
Babban mashawarci na mussaman kan kafafan yada labarai Malam Garaba Shehu ne yana bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Malam Garba Shehu na maida maratani kan korafe-korafen da wasu ‘yan jam’iyyar APC suke zaton cewa shugaban Muhamadu Buhari zai yi amfani da karfin mulkin sa wajen sauya sakamakon zabe a wasu jihohin kasar nan.
Haka zalika Mashwarwacin na shugaban kasa ya gargadi shugabanin siyasa da suke kalaman batanci yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INCE zata gudanar da zabe da bai kammala ba a wasu jihohin kasar nan.
A cewar Garba Shehu wasu tsofafin shugabanin kasar nan kan tsuma baki kan zabe da bai kammala ba, a don hakan ne wasu magoya bayan da ran su ya bacci suke tunanin cewa shima shugaban Muhamamdu Buhari na aikata hakan, sai dai shugaban Muhammadu shi na daban ne.
Ya ce kundin tsarin mulkin kasar nan bai bawa shugabanin kasar nan karfin iko ba, Akan haka ne Garaba Shehu ya bukaci mayo bayan jam’iyyr APC a jihohin da za’a yi zaben da bai kammala ba, da su dage wajen samun kuri’u daga al’ummar dake suke jagoranta,mai makon zaton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amfani da karfin sa don amfani da hukumar zabe don ganin an murde zaben.