Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar dan kasar Lebanon da sace

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar kano ta tabbatar da mutuwar Dan Kasar Lebanon din nan da masu garkuwa da mutane suka sace lokacin da suke tsaka da gudanar da aikin gadar shataletan Dangi ranar Talatar da ta gabata.

Kakakin Rundunar Yan’sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya tabbatarwa manema labarai cewa an tsinci gawarsa  ne a kan titin zuwa Maiduguri a daren jiya Alhamis.

DSP Abdullahi Haruna ya kuma kara da cewa tuni suka mika gawar zuwa Asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin gano Musabbabin mutuwar tasa.

Rahotanin sun bayyana cewar tuni iyalan mammacin suka samu labari kuma har sun fara shirye-shiryen mayar da gawar zuwa kasar su.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai wasu ‘yan nindiga da ba a san ko suwaye ba suka bude wa ma’aikatan dake aiki a gadar shataletalen Dangi wuta, yayin da suka sace mutumin, nan take kuma suka kashe direban sa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!