Labarai
Fadar shugaban kasa ta haramta ayyukan kungiyar ‘yan uwa musulmi
Fadar shugaban kasa ta ce, haramta ayyukan kungiyar ‘yan uwa musulmi wato Islamic Movement in Nigeria, ba ya nufin haramta addinin Shi’a kwata-kwata a kasar nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.
Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar, ya ce, sauran mabiya addinin Shi’a masu son zaman lafiya da ba sa bangaren kungiyar ‘yan uwa musulmi, za su ci gaba da gudanar da harkokin su bisa tsarin doka ba tare da tsangwama ba.
A cewar Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar dai, haramtawar zai taimaka gaya wajen gudanar da tarzoma da kashe mutane da lalata dukiyoyin gwamnati da na al’ummar da ba su ji ba su gani ba.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya kuma ce, babu kanshin gaskiya cikin zargin da kungiyar ta ‘yan uwa musulmi ta yi na cewa, an haramta ma ta yin addini, yana mai cewa; gwamnatin shugaba Buhari ba za ta haramtawa mabiya Shi’a gudanar da Sallah da ziyartar kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajji ba.
Haka zalika Malam Garba Shehu ya kuma zargi mabiya Shi’ar da yada farfaganda don neman jama’a su tausaya musu sannan su kautar da hankulan duniya game da irin ta’addanci da suke aikatawa a kasar nan musamman wajen kaiwan hari ga sojoji da kashe ‘yan sanda da ‘yan hidimar kasa ba ya ga lalata dukiyoyin jama’a, da na al’umma da ba su ji ba ba su gani ba.