Labarai
Fadar Shugaban Kasa ta musanta sauke George Akume daga mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayya

Fadar Shugaban Kasa ta musanta rahotannin da ke yawo cewa an sauke Sanata George Akume daga mukaminsa na Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).
A wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ya bayyana cewa babu wani sabon nadi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, yana mai cewa rahotannin da ke yawo kan sauke Akume “labaran karya ne.
Onanuga ya tabbatar da cewa shugaban kasa na ci gaba da kasancewa a kasar Saint Lucia, kuma bai yi wani sauyi ba a cikin mukaman gwamnati.
Fadar shugaban kasa ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan jita-jita da ake yadawa a kafafen sada zumunta
You must be logged in to post a comment Login