Labarai
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cire naira biliya daya na rarar man fetur
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin da jam’iyyar PDP ta yi na cewa, dala biliyan daya kudaden da ta cira daga asusun rarar danyen man fetur (ECA), ta yi amfani da shi ne wajen babban zaben kasa da ya gudana.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.
Sanarwar ta ruwaito Malam Garba Shehu na cewa, jam’iyyar PDP ta dauka cewa, kowane gwamnati irin halin ta yake, wajen wawushe dukiyar al’ummar kasa, a don haka ya bukaci jam’iyyar da ta kasa kunne ta saurari yadda aka sarrafa kudaden.
A cewar Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar, sanan-nen abune, gwamnatin shugaba Buhari, ta biya gwamnatin kasar Amurka, dala miliyan dari hudu da casa’in wajen sayo jiragen sama na yaki, samfarin Super Tucano guda goma sha biyu.
Malam Garba Shehu ya kuma ce, ko a baya-bayan nan, an sayo kayayyakin yaki na soji wadanda a bayyane suke, al’ummar kasar nan sun ga lokacin da aka kawo su, kuma ya zuwa yanzu, jimillan abinda aka kashe cikin kudin shine dala miliyan dari takwas da tamanin.
A jiya lahadi ne dai jam’iyyar PDP ta cikin wata sanarwa, ta bukaci shugaba Buhari da ya yi karin haske ga al’ummar kasar nan, kan yadda gwamnatin sa, ta sarrafa dala biliyan daya da ta cira daga asusun rarar danyen man fetur a shekarar dubu biyu da goma sha bakiwa, da nufin amfani da shi a harkokin tsaro.