Labarai
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kalaman da jam’iyyar PDP ke yi hutun shugaba Buhari
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kalaman da jam’iyyar adawa ta PDP ke yi cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara hutun kwana 10 ne a yau domin kawo al’amura da za su sanya rudani cikin al’amuran kasar nan wadanda ba suyi dai-dai da tsarin mulki ba.
Mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan da yammacin jiya Alhamis, inda ya ce wannan zance bashi da tushe ballantana makama.
A cewar Garba Shehu ya riga ya mika ragamar shugabancin kasar nan ga mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo ba tare da jin ko dar ba, abin da jam’iyyar ta PDP ta kasa yi a tsahon shekaru goma sha shida da ta kwashe ta na mulki.
Ya kara da cewa domin a cire wa mutane shakku, ya kamata jama’a mutane su san cewa mataimakin shugaban kasa wanda zai rike kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasar, cikakken lauya ne da ke da lambar girma ta SAN wanda kuma ke yaki wajen ganin al’umma sun samu yancin su a ko ina suke.
A don haka bai kamata jam’iyyar adawa ta PDP ta yi tunanin cewar gwamnatin tarayya za ta kwaikwayi irin abinda suka yi a zamanin suna kan mulki ba.