Connect with us

Labarai

Fadar Shugaban Najeriya ta yi kakkausan martani ga Peter Obi

Published

on

Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da martani ga Peter Obi, bayan kalamansa na sukar tafiye-tafiyen Tinubu zuwa ƙasashen waje, tana mai cewa Obi abinda yake faɗa zallar siyasa ne kawai.

Mai taimaka wa shugaba Tinubu kan harkokin sada zumunta, Dada Olusegun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya kare ziyarar da shugaban ƙasar ya kai taron Africa CEO Forum da aka gudanar a Kigali na ƙasar Rwanda.

Ya ce Tinubu ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa Rwanda da ta ƙunshi manyan attajirai da shugabannin masana’antu na kasar nan, ciki har da Aliko Dangote, Abdul Samad Rabiu, Tony Elumelu, Jim Ovia da kuma Wale Tinubu da dai sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!