Labarai
Sarkin Musulmi a Najeriya ya bukaci a fara duba watan Zulhijja a gobe Lahadi

Mai Alfarma sarkin musulmi kuma shugaban majalisar koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya bukaci al’ummar musulmi a fadin kasar nan da su fara duba jinjirin watan Zulhijja na shekarar 1447 a ranar Lahadi 17 ga Mayun da muke ciki.
Hakan dai na cikin sanarwar da kwamitin harkokin addini na majalisar Masarautar Sokoto ya fitar ta hannun Shugabanta, Farfesa Sambo Wali Junaidu, inda ta ce ranar ta yi daidai da 29 ga watan Zulki’ida na shekarar 1447 bayan hijira.
Sanarwar ta kuma bukaci duk wanda ya ga jinjirin watan da ya sanar da Hakimi ko Dagaci mafi kusa domin isar da bayanin ga Sarkin Musulmi don daukar matakin da ya dace.
You must be logged in to post a comment Login