Labarai
Faransa za ta tallafawa Kano don bunƙasa ilimi
Gwamnatin ƙasar Faransa ta yi alƙawarin tallafawa Kano wajen bunƙasa Ilimi.
Jakadan Faransa a Najeriya, Jerome Pasquier ne ya bayyana haka ranar Litinin a Kano, yayin karɓar daliban Kano da suka je ƙaro karatu Faransa.
Jakadan ya ce, shiri ne da Gwamnatin Kano ke yi na ɗaukar nauyin ɗaliban tare da haɗin gwiwar Faransa.
Ya ce, za a faɗaɗa shirin a nan gaba domin manyan makarantun jihar Kano su amfana.
A nata jawabin Kwamishiniyar Ilimi mai zurfi ta jihar Kano, Dakta Mariya Mahmud Bunkure, ta ce, zuwa yanzu haka ɗaliban Kano sama da 60 ne suka ci gajiyar shirin.
Gwamnatocin biyu sun ƙara sabinta yarjejeniyar shirin zuwa shekarar 2024, tare da fatan ɗorewarta a gaba.
You must be logged in to post a comment Login