Labarai
Farashin gangar mai ya tashi a kasuwar duniya
Farashin gangar ɗanyen mai karon farko cikin ya tashi zuwa dala saba’in da ɗaya da santi ashirin da takwas a karon farko cikin wannan shekara.
Wannan na zuwa ne gabanin taron da ƙungiyar ƙasashe masu arziƙin man fetur (OPEC) za ta yi a ranar Alhamis mai zuwa.
Tun farko dai ƙasashen kungiyar ta OPEC da sauran ƙasashen da ke da arziƙin man fetur da ba sa cikin ƙungiyar sun ƙi amincewa su ƙara adadin man da suke fitarwa.
Rahotanni sun ce, a ranar larabar makon jiya an riƙa sayar da mai samfarin Brent a kan dala sittin da uku da santi casa’in da takwas.
You must be logged in to post a comment Login