Kasuwanci
Farashin kayayyaki a kasuwar ‘Yankaba ba yabo ba fallasa – Inji masu sayayya
A ci gaba da kawo muku yadda farashin kayayyaki ya ke a lokacin azumi a wasu daga cikin kasuwanni da ke birnin Kano, a yau wakiliyar mu Maryam Isa Gunduwawa, ta ziyarci kasuwar ‘Yan kaba.
Kamar yadda a rahoton da muka kawo muku kan farashin kayayyaki a wasu kasuwanni a jiya, ya nuna yadda ake samun karin farashin, sai dai a kasuwar ‘Yankaba da ke karamar hukumar Nassarawa da muka ziyarta da safiyar yau, lamarin ya sha bamban.
Domin kuwa a zantawa da muka yi da wasu daga cikin mutanen da suka zo kasuwar don sayayya, akasarin-su sun bayyana cewa, farashin ya sauko idan aka kwatanta da kafin fara azumi.
Sai dai wasu na da ra’ayin cewa har yanzu da sauran rina a kaba, domin a wasu nau’ikan kayayyakin har yanzu farashin su hauhawa su ke yi.
Misali: farashin shinkafa, wake, doya duk basu sauya ba a kasuwar, amma kayan miya da na marmari har ma da dankalin turawa duk farashinsu sun tashi.
Muhammad Abdulkarim Kazodi shine mataimakin shugaban kungiyar masu sai da dankalin turawa ta kasa reshen jihar Kano, ya ce dalilin da ya sa farashin dankalin turawa ya tashi a kasuwar yana alaka ne da karancin sa ba wai azumi ne ya janyo tashin farashin ba.
Al’umma dai na fata ‘yan kasuwar za su rika la’akari da falalar da ke cikin wata Ramadan don sassautawa jama’a.
You must be logged in to post a comment Login