Coronavirus
Farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabi a duniya – Majalisar Dinkin Duniya
Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya (FAO), ta ce, farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabi a duniya.
A cewar hukumar ta FAO wannan shine watanni goma a jere da ake samun hauhawar farashin kayayyakin abincin.
Alkaluman da hukumar ta fitar a ranar alhamis sun nuna cewa, a watan jiya na Maris, farashin kayayyakin abinci ya haura da a kalla kaso biyu da digo daya wanda rabon da a ga haka tun a shekarar 2014.
Rahoton hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniyar ya kuma nuna cewa, kayayyakin lambu, man girki, madara, sune kan gaba da farashin su ya karu.
Hukumar ta kuma alakanta lamarin da ci gaba da yaduwar cutar corona wadda ta ce cutar ta taka rawa wajen kara ta’azzara halin da ake ciki, musamman yadda mabukata su ka kara yawa, a bangare guda duniya ke fama da karancin abinci.
You must be logged in to post a comment Login