Kiwon Lafiya
Farfesa Wole Soyinka:Kalaman kire da bata suna na barazana da bil Adama
Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa yada kalaman kire da na bata suna a Yanzu haka ya zama babbar barazana ga bil’adama kuma hakan ma ka iya tayar da yakin duniya na uku.
Farfesa Wole ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da kafar yada labarai ta BBC ta shirya kan hanyoyin da za’a bi na magance yada kalaman kire da na bata suna da ya gudana a Abuja.
Ya kuma kara da cewa kafin kalaman kire su yi sanadiyyar barkewar yakin duniya na uku ya zama wajibi a bi duk hanyoyin da ya kamata don magance su musamman a kasa irin Najeriya.
Farfesa Wole ya kuma nuna takaicin sa kan yadda ake yawan alakanta kalaman da wasu marasa kishin kasa ke kirkirowa da a gareshi.
Inda ya buga misali da cewa ko a shekarun baya ma an alakanta wani labaran karya garshi shi, inda aka ce wai ya bayyana matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin jahila.
Sannan ya kara da cewa ko a shekarar da ta gabata ma ya sha cin karo da maganganu musamman a kakafen sadarwa da ake alakan ta shi da su, wanda hakan ya sanya mutane da dama su ka rika kalubalantar sa da hakan.