Kiwon Lafiya
Farfesa Yemi Osinbajo ya ce an wawushe dala biliyan uku tsakanin NNPC da wasu kamfanonin hakar mai
Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, ya ce; an wawushe dala biliyan uku cikin wata yarjejeniya da kamfanin mai na kasa NNPC ya yi da wasu kamfanonin hakar mai na kasashen ketare.
Da yake jawabi yayin wani taro da aka shirya domin tattauna halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki a Abuja, Osinbajo ya ce, lamarin ya fau ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ya ce, abin takaici, a wata badakalar da aka yi daf da zaben shekarar dubu biyu da sha biyar, an wawushe naira biliyan dari, yayin da a hannu guda kuma aka sake kwashe wasu kudaden dala miliyan dari biyu da casa’in da biyar.
Farfesa Yemi Osinbajo, ya kuma ce; ga shugaba da ya samu jagorancin kasa da aka yi kaca-kaca da ita wajen wadaka da dukiyar al’ummarta, jajirtaccen shugaba bane kawai zai iya lallabata har ta kai halin da kasar nan ke ciki a yanzu.
Ya kara da cewa, gwamnatin su na iya kokarinta domin ganin ta samu nasarar farfado da tattalin arzikin kasar nan.