Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NFF ta fara biyan albashin ma’aikatan dake bin ta bashi

Published

on

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF Amaju Pinnick ya ce an biya mai horas da kungiyar kwallon ta kasa Super Eagles Gernot Rohr albashin wata biyu a cikin albashin watanni biyar da yake bin hukumar.

Pinnick ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa ta musamman da jaridar Punch a yau Litinin.

Ya kuma ce shima mai horas da masu tsaron ragar Super Eagles Alloy Agu wanda yake bin albashin watanni ashirin da biyu ya karbi na watanni tara.

Pinnick ya ce yanzu haka hukumar ta dora damba wajen ganin ta biya dukkannin ma’aikatanta da ke bin ta bashi kamar yadda tayi alkawari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!