Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

FIFA za ta duba yuwuwar gudanar da gasar cin kofin Duniya duk bayan shekaru 2

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta gayyaci masu horar da ‘yan wasan kwallon kafa na kasashe 211, don tattaunawa kan yadda za a sauya fasalin gudanar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekaru 2.

Kamar yadda FIFA ta sanar a ranar Litinin 18 ga watan Oktobar 2021, ta ce tana son a bayar da shawara kan yadda ya kamata a tsara gasar da kuma gyara kalandar wasannin cin kofin Duniya.

Za dai a gudanar da taron ne ta dandalin sadarwa na zoom daga yau Talata 19 zuwa ranar Alhamis 21 ga watan Oktobar 2021.

Tsohon mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma shugaban bunkasa harkokin kwallon kafa na hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, Arsene Wenger ne zai jagoranci tattaunawar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!